Kwamitin sulhu na MDD ya bada umarnin tura rundunar 'Yansanda ta kasa da kasa mai karfin jami'ai 228 zuwa Burundi, domin hana keta 'yancin Bil'Adama da samarda daidaito domin a gudanarda shawarwarin sulhu tsakanin al'umar kasar.
Kwamitin ya bayyana fatar kasancewar 'Yansandan zai samarda yanayi mai kyau domin a yi shawarwari masu ma'ana domin kasar ta magance cikas da ta shiga ta fuskar siyasa.
"Ganin karuwar tashe tashen hankula da zaman dar dar, tilas ne kwamitin sulhu ya sami wakilci a kasa, domin yayi hasashe da kuma tabbatar lamari mai muni bai auku ba a Burundi," inji jakada Francois Delattre, wanda tawagarsa ce ta rubuta kudurin na kwmaitin sulhu.
Tarzoma ta barke ne a kasar a cikin watan Afrilun bara, bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya nemi yin tazarce, mataki da jama'ar kasar da dama suka dauka a zaman wanda ya sabawa tsarin mulkin kasar. Tun bayan haka an kashe fiyeda mutane 450, yayinda wasu dubu metan da saba'in su gudu daga kasar zuwa kasashe makwabta.
Ahalinda ake ciki kuma, MDD ta kara wa'adin aikin kiyaye zaman lafiya da take yi a Sudan ta kudu har zuwa 12 ga watan Agusta mai zuwa, a dai dai lokacinda ake samun karin rahotannin barkewar sabbin tarzoma a jahohi dake kudancin kasar.Gobe lahadi ne ake sa ran wa'adin na yanzu zai kare. Wannan matakin na dan gajeren lokaci ne kafin manyan kasashen duniya su tantance matakin da zasu dauka nan gaba.