'Yan Adawa Na Yunkurin Tsige Firai Ministan Jamhuriyyar Nijar

Majalisar Dokokin Kasar Nijar

Zazzafar muhawara ce ta barke a zauren majalisar dokokin jamhuriyyar Nijar, a lokacin zaman da ta shafe sa'o'i fiye da 17 ta na gudanarwa a wunin jiya Alhamis.

Majalisar dokokin ta zauna da nufin raba gardama tsakanin masu rinjaye da ‘yan adawa, wadanda suka zo da bukatar tsige Firai Minista Birgi Rafini, daga mukaminsa saboda abinda suka kira rashin gamsuwa da kamun ludayinsa, amma a karshe masu rinjaye sun yi nasara bayan kada kuri’u.

A jawabin wasu 'yan majalisar, da suka hada da Hon. Idrissa Maidaji dan jam'iyyar PNDS tarayya mai mulki, wanda yace wasu ne suke neman nuna wa duniya akwai rashin gaskiya da damuwa a fannin demokradiyyar Nijar.

A cewar Hon. Korone Masani, jam’iyyun adawa daga yanzu sun kaddamar da gwagwarmaya sai sun ga abinda ya ture wa buzu nadi.

Hare haren ta’addancin da ake fuskanta a Nijar na daga cikin matsalolin da ‘yan hamayya ke ganin sun faskari gwamnatin wannan kasa, to amma da yake maida martani Firai Minista Birgi Raffini, na ganin rashin dacewar tallata matsalar tsaro.

A rahoton wakilin muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Adawa Na Yunkurin Tsige Firai Ministan Jamhuriyyar Nijar