'Yan Adawa A Nijar Sun Kushewa Tayin Shiga Gwamnatin

NIGER: 'Yan adawana Jamhuriyar Nijar da suka kushewa ttayin shiga gwamnati

Ba yau ba ne shugaban kasar Nijar ya taba kiran 'yan adawa da su shiga gwamnatinsa, kuma duk lokacin da ya yi haka, ya kan raba kawunan 'yan adawan har su yi watsi da adawa domin baraka a tsakaninsu.

'Yan adawa sun ce idan sun shiga gwamnati da wa za'a bar talakawa saboda su suka zabi shugaban gwamnati da wadanda suke gwamnati da kuma 'yan adawa domin su kare talakawan.

'Yan adawa su ne suke da bakin magana, su kare muradun talakawa ba su shiga gwamnati ba domin su rasa bakinsu. Su a jam'iyyar MNSD mai adawa sun fadawa shugaban kasar Mahammadou Issoufou ya kai tayin kasuwa.

Issoufou Mahammadou da Frayim Ministansa Birji Rafini

Tayin da shugaban yayi can baya a wa'adin milkinsa na faro ya yi sanadiyar barkewar baraka a jam'iyyar ta MNSD har wasu manya manyanta suka shiga gwamnati kuma har yanzu ana damawa dasu.

'Yan adawan sun ce duk wanda ya gaji da adawa sai ya rubuto wasikarsa cewa ya bar adawa ko ya fice daga jam'iyyar.

Ga rahoton Souley Moumouni Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Adawa A Nijar Sun Kushewa Tayin Shiga Gwamnatin - 1' 59"