A yayin zaman dirshan da matan jam’iyyun adawa suka gudanar a kofar cibiyar jam’iyar RDR Canji da nufin matsa wa hukumomi lamba don ganin sun sallami shugabannin ‘yan adawar da aka kulle a kurkuku a makon jiya, jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla don tarwatsa dandazon wadannan mata kafin daga bisani su yi awon gaba da wasu shugabanninsu.
Alhaji Doudou Rahama, wanda ya shafe kwanaki uku a hannun ‘yan sandan farin kaya kafin a sallame shi a jiya, ya yi tur da faruwar wannan al’amari a kasar da ake bin tsarin dimokuradiyya.
Kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani ba a game da dalilan kama wadannan mata; to amma a cewar kakakin jam’iyyar PNDS mai mulki, Assoumana Mahamadou, rashin mutunta doka ne mafarin daukar wannan mataki.
A washegarin barkewar zanga zangar watsi da sakamakon zabe, ofishin alkali mai kare muradun hukuma a kotun Yamai, ya bada sanarwar cafke daruruwan mutane da ake zargi da hannu a wannan al’amari, cikinsu har da wasu jagororin jam’iyyun adawa da suka hada da tsohon Firaminista Hama Amadou da Janar Moumouni Boureima mai ritaya, mafarin fitowar wadannan mata a jiya. Alhaji Doudou Rahama na cewa zasu ci gaba da wannan gwagwarmaya ta neman ‘yanci.
A daya bangare, wata tawagar wakilan kungiyar Tarayyar Turai da CEDEAO da Majalisar Dinkin Duniya (MDD} ta gana da dan takarar hamayya Mahaman Ousman da yammacin ranar Litinin a birnin Yamai, inda ya yi masu bayani a game da dalilansa na watsi da sakamakon zaben 21 ga watan Fabrairu, sannan ya danka masu kofin takardun dake kunshe da hujjojin da ya gabatar wa kotun tsarin mulkin kasa, a bisa zargin an tafka magudi. Yana mai ce da su shi ya yi nasara a wannan zabe, sai dai bangarorin ba su yi wa ‘yan jarida bayani komai ba a karshen wannan ganawa.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma ya aiko da rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5