Watakila kafin a kai lokacin shagulgullan Kirsimetin wannan shekara, an gama shafe birnin Aleppo na kasar Syria daga doron kasa – muddin Syria da Rasha basu ja burki ga fatattakar da suke yi wa birnin da jiragensu na yaki ba, a cewar manzon MDD na musammam na Syria, Staffan de Mistura.
WASHINGTON, DC —
A jiya ne jami’in na MDD yake fadar cewa Allah kadai Ya san yadda mutanen birnin na Aleppo su 275,000 suke ci gaba da iya jurewa wannan masifar hare-haren bama-bamman da ake ta sakar musu ba kakkautawa, amma dai yana jin ba zasu iya dadewa suna jurewa masifar ba.
Saboda haka ne Mr. Mistura yake cewa idan har aka ci gaba da kai irin wannan farmakin kan garin na Aleppo, to dubban mutane zasu mutu, dubbai zasu samu raunukka, sauran kuma su karkare a matsayin ‘yan gudun hijira.
Shima garin Homs, wanda shine birni na ukku wajen girma a kasar Syria, haka aka yi mishi shekaru 3 da suka wuce, inda aka hallaka dubban mazaunansa a lokacin yakin da aka yi tsakanin mayakan ‘yan adawa da sojan dake biyayya ga shugaban Syria din, Bashar al-Assad.