Ana sa ran cewa nan bada dadewa ba za a tabbatar da shi a hukumance akan wannan mukamin.
Bayan an jefa kurji’un da kusan duk na bangare daya ne a jiya a zauren babban kwamitin zartaswa na MDD, aka fahimci cewa wannan tsohon dan siyasa kuma jami’in diplomasiyar ya yi galaba da kuru’u 13 da ya samu, kuma babu wanda ya nuna rashin amincewa koda yake akwai kasashe biyu da suka kaucewa jefa kuri’unsu.