Muddun jama’a ba su daina barin muhallansu cikin yanayin da ke ba da sauro mafaka ba, to duk wani kokarin da hukumomi ke yi na yaki da zazzabin jizon sauro ba zai yi cikakken tasiri ba, a cewar wani likita dan Najeriya mai wata ziyarar aiki a nan Amurka, mai suna Dr. Mustapha Sani.
Da abokin aikinmu Ladan Ibrahim Aywa ya tambaye shi gaskiyar rahotannin da ke cewa Najeriya na sahun gaba a jerin kasashen da cutar maleriya ta fi kashe mutane, sai Dr. Sani y ace hakan na iya zama gaskiya idan aka lura da yadda jama’a ke kin tsabtace muhallai da sauran nau’ukan dabi’u na kazantar muhalli da rashin kula. Dr. Sani ya ce, “Idan har ka ji an ce haka, to akwai bincike mai zurfi ne da aka yi wanda ya tabbatar da hakan. Tabbas na san Najeriya ta na daya daga cikin kasashe masu fama da wannan cuta ta maleriya. Amma b azan iya sanin ko lallai ita ce ta daya ko kuma cikakken matsayinta ba.” Da Ladan ya tambaye shi mafita idan hakan ya zama gaskiya, sai Dr. Sani ya ce mafita it ace kamar yadda aka saba, da gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu su cigaba da hada kai da kuma ba da himma wajen yaki da cutar. Y ace su ma sauran jama’a akwai rawar da ya kamata su daka, kamar kawar da duk wani kwantaccen ruwa da datti, wadanda su ne sauran ya fi son zama ciki.
Da Ladan ya tambaye shi ko kokarin da aka sha yi a baya wanda ya hada har da bayar da gidajen sauro bai yi tasiri ba Kenan, sai ya ce ba wai bai yi tasiri ba ne. yaki da sauron ne ke da matukar wahala. Y ace ba aikin Ma’aikatar Lafiya ba ne kawai. Har ma da Ma’aikatar Muhalli da dai sauransu. Ya ce a yayin da hukumomi ke iya bakin kokarinsu, matukar dai jama’a ma ba su bayar da tasu gudunmowa ba, ba za a ci nasara.
Your browser doesn’t support HTML5