Yak’i da fataken mata a Najeriya da Cote d’Ivoire

Kungiyar kare hakkokin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce a tashi haik’an a yak’i ‘yan k’asashen Cote d’Ivoire da Najeriya masu fataucin mata don sa su karuwanci.

Kungiyar kare hakkokin Bil Adama ta Human Rights watch ta ce dole ne kasashen Cote d’Ivoire da Najeriya su yi aiki wurjanjan don ceton matan da ake tursasawa shiga karuwanci.

A cikin rahoton da ta gabatar a jiya alhamis, kungiyar Human Rights Watch ta ce ana yaudarar mata da ‘yan matan k’asar Najeriya a kai su k’asar Cote d’Ivoire bisa alk’awuran sama mu su ayyukan yi da kuma ba su horo. Daga su isa kasar ta Cote d’Ivoire sai a mik’a mu su hulunan mazakuta sannan a ce mu su, su fara karuwanci.

Mai gudanar da bincike, Matt Wells ya ce da yawan matan kan ji tsoron cewa idan su ka k’i bin umarnin, za a taba lafiyar su ko ta iyalan su.

Kungiyar kare hakkokin Bil Adama ta Human Rights Watch ta gano cewa yawancin wadanda abun ke rutsawa da su ‘yan shekaru 15 ne zuwa 17 kawai.

Yak’i da fataken mata a Najeriya da Cote d’Ivoire

Wells ya ce ofishin jakadancin Najeriya ya taimakawa d’imbin ‘yan mata sun koma gida a bana. Amma galibi , ofishin jakadancin na shiga cikin maganar ne idan wadda ta samu kan ta a cikin irin wannan hali ta samu hanyar gudu kuma ta nemi taimako.

Kungiyar ta kare hakkokin Bil Adama na kira ga jami’an gwamnatocin Najeriya da na Cote d’Ivoire da su rika d’aukan matakan rigakafi, suna yin bincike akan fataken matan kuma su dakatar da kwararar sabbin matan da abun ke rutsawa da su.