Nijeriya ta ce an kashe wasu ‘yan sanadanta a Arewacin kasar, a wani al’amarin da ba zai rasa nasaba ba da sake bullar wata kungiyar masu tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci.
Jami’an gwamnati sun fadi yau Jumma’a cewa wasu mutane su hudu, saye da bakaken tufafi bisa babur sun bindige wasu jami’an yan sanda biyu a daren Laraba a babban birnin jahar, Maiduguri.
Su ka ce an kashe dan sanda na uku ne a wani wurin dabam amman a wannan daren kusa da gidan gwamnan jihar Yobe.
Jami’an yan sanda sun ce ana kyautata zaton yan bindiga dadin ‘yan kungiyar Boko Haram ne.
A watan Yulin da ya gabata ne dai yan kungiyar ta Boko Haram su ka kai hari kan ofishin yan sanda, da majami’u da kuma gine-ginen gwamnati a Arewacin Nijeriya.
Wannan harin ya janyo martani mai tsanani daga ‘yan sanda da sojoji. Sama da mutane 700 ne dai akak hallaka.