A kokarin da hukumomin Najeriya keyi na yaki da cutar shan inna an kaddamar da allurar rigakafin cutar karo na shida a jihar Neja
A yakin da hukumomin Najeriya keyi da kawar da cutar shan inna daga kasar an kaddamar da bada allurar rigakafin cutar karo na shida a jihar Neja.
Hukumomin jihar Neja dai sun dage matuka game da kawar da cutar a tsakanin jama'a inda aka sanar cewa za'a hukunta duk wanda ya ki a ba dansa rigakafin ko kuma ya doki masu aikin bada allurar rigakafin a jihar.Alhaji Yusuf Tagwai kwamishanan kananan hukumomi da masarautu wanda ya wakilci gwamnan jihar a wurin bikin a Beri cikin karamar hukumar Mariga shi ne ya sanar da hakan. Ya kara da cewa bayan an hukunta mutum idan ba dan jihar ba ne za'a koreshi daga jihar. Shi ma Sarkin Sudan din Kontagora Alhaji Saidu Namaska ya ce duk wanda ya hana a ba 'ya'yansa allurar rigakafi za'a kulleshi idan dankasa ne. Idan kuma zuwa ya yi za'a fitar da shi.
Ita karamar hukumar Mariga ta fito da wata dabarar bada kyautar sabulu da gidan sauro ga duk matar da ta kawo 'ya'yanta karbar allurar rigakafin kamar yadda shugaban karamar hukumar Mariga Alhaji Kabiru Tanka ya bayyana. Ya ce duk matar da ta samu kyautar sabulu da gidan sauro zata koma ta shaida wa 'wasu abubuwan da ta samu sabili da kawo 'ya'yanta karbar allurar. Ta haka ne za'a samu a jawo hankalin mata su amince da allurar.
Da alama dabarar ta karamar hukumar na raba sabulu da gidan sauro ta samu shiga domin wasu mata da aka zanta da su sun yi godiya da abubuwan da aka basu da alkawarin cigaba da kawo 'ya'yansu domin a yi masu allurarar.
Ana zaton za'a yiwa yara kusan miliyan biyu a wannan shirin allurar rigakafin da za'a fara daga shida ga wannan watan Yuli zuwa tara ga watan.
Mustafa Nasiru Batsari ya yi karin bayani a wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5