Yaki da cin hanci da rashawa na Najeriya ya sa wani dan diflomasiyar Amurka wallafa littafi a kai.
Abun da ya zaburashi rubuta littafin shi ne yawaitar satan mutane a sassan duniya daban daban domin samun kudin fansa da muggan mutane da 'yan ta'adda keyi. Ya ce hakan na kawowa 'yan Najeriya da 'yan Amurka matsala.
Akwai 'yan Najeriya da dama da suke wallafa littafai akan alamuran Najeriya amma babu amurkawa masu rubutu akan Najeriya, inji ba'amariken.
Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Alhaji Nuhu Ribadu ya halarci taron. Ya ce wanda ya wallafa littafin yana cikin gwamnatin George Bush kuma sun taimaka ma hukumarsa wajen samun nasarori da yawa.
Akan salon yaki da cin hanci da rashawa na Shugaba Muhammad Buhari, Alhaji Nuhu Ribadu ya ce duk duniya ta jinjina masa ya yadda yake yakin. Injishi yaki da cin hanci da rashawa ba karamin aiki ba ne saboda kusan ana yaki da kowa ne. Masu iko da arziki basu bari sai sun yi fada da yakin.
A saurari rahoton Saleh Shehu Ashaka da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5