Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Jinjinawa Sojojin Sama Na Najeriya Don Kera Jirgi Maras Matuki


‘Tsaigumi’
‘Tsaigumi’

Air Commodre Baba Gamawa yace galibin kayayyakin da aka kera "Tsegumi" dasu a cikin Najeriya aka yi su.

Air Commodore Baba Gamawa mai riyata yayi kira ga 'yan Najeriya da su yi adalci ga shugabanni, kullum idan suka ga wani abu da ba su fahimta ba, su nemi bayani, maimakon hawa kafofin sada zumunta suna sukar shugabanni.

Air Commodore Gamawa, yace dukkanin ko mafi yawan kayayyaki da rundunar mayakan sama na Najeriya suka yi amfani da shi wajen kera jirgin saman nan mai shawagi da bashi da matuki da ake kira "Tsegumi" a Najeriya aka samar da kayayyakin. Gamawa yace sabanin irin rade-radi da ake yi a shafukan sada zumunta.

Air Commodore Baba Gamawa yace, sojojin saman Najeriya suna da kwarewa kuma idan ana ci gaba da basu hadin kai da goyon baya, za'a a ga irin kawarewa da baijintar da Allah Ya ba su.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG