Yaki da Boko Haram Shi ne Abun dake Gaban Sojojin Najeriya - Janar Buratai

Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai

Babban hafsan sojojin Najeriya ya jaddada cewa babu ko tantama gwagwagwan da su keyi da 'yan ta'adan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya shi ne abu mafi mahimmanci da suka sa gaba saboda cimma wa'adin da shugaban kasa ya basu wanda yanzu saura mako daya kawai..

Janar Buratai yace saboda cimma wa'adin ya bada umurni daban daban domin karfafa ayyukansu da suka sama taken "Operation Lafia Dole"

Yanzu da wa'adin da shugaban kasa ya ba sojojin su murkushe 'yan Boko Haram, Birigedia Rabe Abubakar kakakin hedkwatar sojojin ya bayyana halin da ake ciki. Yace suna kara karfi da karfe domin su tabbatar sun gama da 'yan ta'adan cikin wa'adin da aka basu.

Inji Birigerdia Rabe sun karya karfin 'yan ta'adan. Duk inda suke an fatattakesu. Sojojin sun tarwatsasu suna cikin yunwa yadda ba zasu iya shirya wani aikin ta'adanci ba kamar da. Abun da ya rage masu shi ne rugawa kauyuka suna satar abinci. Ko wannan ma sojojin zasu shawo kansa.

Jihar Yobe na daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya yi kamari. Gwamnatin jihar tuni ta nuna gamsuwarta da kwazon dakarun sojojin Najeriya. Kwamishanan yada labaru na jihar Alhaji Yerima Bularafa yace sun dade basu samu irin tashin hankalin Boko Haram ba irin na shekarun baya. Da ba'a dadewa ba'a samu tashin bamabamai ba. Yace wannan shi ne alamar samun nasara. Kananan hukumomi biyu da 'yan Boko Haram suka mamaye a jihar tuni sojoji suka kwatosu. Mutane da yawa dake gudun hijira sun koma gidajensu.

Air Kwamanda Tijjani Baba Gamawa wani kwararre kan sha'anin aikin soja yace yanzu kowa ya san cewa rundunar sojojin Najeriya tayi rawar gani. Su kuma dake yankin da 'yan Boko Haram suka daidaita sun san an samu zaman lafiya.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Yaki da Boko Haram Shi ne Abun dake Gaban Sojojin Najeriya - Janar Buratai - 3' 00"