Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Rasa Jami'anta Biyu a Fafatawarta da 'Yan Boko Haram


Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai
Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai

Cikin kwanaki biyu da suka fafata da 'yan Boko Haram a dajin Sambisa sojojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram arba'in da tara yayin da manyan jami'an sojoji biyu su ma suka rigamu gidan gaskiya.

Rundunar sojojin Najeriya tace ta kashe kimanin 'yan Boko Haram 49 a cikin kwanaki biyun da suka gabata yayinda wasu manyan sojoji suka rasa rayukansu a fafatawar da suka yi.

Manjo Janar Yushau Abubakar shi ne babban kwamandan sojojin runduna ta bakwai dake yaki da 'yan Boko Haram a arewa maso gabas wadda kuma take da hekwatarta a Maiduguri.

Janar Abubakar ya shaidawa manema labarai cewa suna samun nasarori akan 'yan ta'adan har ma sun samu kutsawa cikin dajin Sambisa har suka kwato kayan yaki da dama daga 'yan Boko Haram.Sun kuma kubutar da wasu kauyawa da maharan kan yi garkuwa dasu.

A cikin bayaninsa Janar Abubakar yace an yi masu kwantar bauna a kan hanyar Bama zuwa Maiduguri amma sun kubuta kuma sun karkashe maharan da dama. Haka ma lamarin ya wakana a wasu kauyukan da suka fafata da 'yan Boko Haram.

Banda 'yan ta'ada 49 da suka kashe cikin kwana biyu Janar Abubakar yace kullum ba'a rasa kashe 'yan ta'ada biyu ko uku.Sun kakkabe babura da makamai da wasu ababen hawa. Bugu da kari sojojin sun ceto mutane kimanin 150 wadanda suka hada da mata da yara da tsoffi.

Ya kira jama'a da su taimakawa sojoji da tsugunta masu duk abun da suka gani game da 'yan ta'ada da aikin ta'adanci.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG