Wannan gangami da matan suka yi a kauyen kwali da ke yankin babban birnin tarayyar Abuja, can kusa da iyakar jihar Kogi, ya mayar da hankali kan karawa Ungozoma ilimin kula da matan da aka yi wa kaciya lokacin da suka zo haihuwa.
Masana daga hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Abuja sun bukaci jami’an ungozoman su ke garzayawa da irin matan asibiti maimakon karbar harhuwar a gida.
Masanan dai na cewa kaciyar akan yi ta ne da zummar hana matan fasikanci kafin su yi aure, wadda hakan kan juye ya zama babbar illa.
Samun karin irin matan da aka yi wa kaciya a asibitoci ya sanya zama wajibi a shirya irin wannan taro na musamman a karkara, shine jigon jawabin shugaban hukumar kiwon lafiya matakin farko na Abuja Dakta Rilwan Mohammad.
Ya kara da cewa tun lokacin da aka gano cewa Najeriya da wasu kasashe ana yin al’adar, hakan ya sa aka yanke hukuncin kowacce shekara a rika tunawa da shi ana kuma dubawa domin ganin ko an ci gaba da aiwatarwa.
Bincike ya gano cewa kunya na tasiri wajen boye matan da ke dauke da wannan matsala inda su kan ki fitowa fili su bayyana kansu.
Domin karin bayani saurari rahotan Saleh Shehu Ashaka.
Your browser doesn’t support HTML5