Yakan Isar Da Sakonnin Da Sukan Hada Da Wa’azi - Abubakar Abdullahi

Abubakar Abdullahi wanda aka fi sani da Habu jajaye, mawakin hip-hop ne, wanda ya ce ya fara waka ne tun yana karami, sakamakon sha’awa kamar yadda mafi yawan mawakan kan tsinci kansu.

Daga cikin sakonnin da mawaki Habu jajaye kan isar a ta bakinsa, sun hadar da fadakarwa dangane da yadda wasu mawakan kan yi musu kallon cewar su yaraya ne basu da basirar da zasu fito su ma a kara da su.

Har ila yau ya ce yakan isar da sakonnin da suka hadar da wa’azi na yadda wasu mawakan kan yi amfani da kalmomin da basu dace ba, wasu lokutan ma har da zage-zage a wakokinsu ko habaici da sauransu.

A lokacin da Habu ya ce ya fara waka iyayensa basu aminta ba da farko, sai daga bisani suka fahimci cewar sana’ar ce kuma ba abu ne da bashi da kyau ba, hasali ma wata basirar ce da ba kowa ke da wannan baiwar ba.

Ya kara da cewa da dama al'ummar gari a lokacin da suka fara waka ana yi musu kallon marasa abin yi, da basu san abinda suke yi ba, wasu lokutan ma akan yimusu kallon marasa da'a a ta bakin mawakin.

Your browser doesn’t support HTML5

Yakan Isar Da Sakonnin Da Sukan Hada Da Wa’azi - Abubakar Abdullahi 05'34"