A wata hira da ta yi da CNN a jiya Litinin, Sanata Kirsten Gillibrand daga New York tace, ya kamata ya yi murabus saboda wannan zargin na da kanshin gaskiya kuma suna da yawa.Tace ta ga wadannan mata cikin bacin rai yayin da suke tabbatar da faruwar lamarin.
Ta kara da cewa, idan har Trump bai gaggauta yin murabus ba, majalisun kasar zasu gudanar da bincike a kan halayensa kuma su dauki matakan da suka dace a kansa.
Wadannan kalaman sun biyo bayan kiraye-kiraye da Sanata Bernie Sanders dan indinpandan daga Vermont da Jeff Markley dan Democrat daga Oregon da kuma Cory Booker na Democrat daga New Jersey suka yi. Dukkaninsu sun yi kira ga shugaban da ya ajiye aikinsa biyo bayan sanarwar murabus da wakilin jihar Minnesota Sanata Al Franken ya yi bisa zargi zargin batsa da yan mata.
Mata guda uku da suka fito a bara suka zargi Donald Trump da yin lalata da su bada son ransu ba, sun sabonta zarginsa a jiya Litinin, suna cewar lokaci ya yi da ya kamata majalisun Amurka su gudanar da bincike a kan shugaban kasa, ganin irin matakai da ake dauka a kan wasu Amurkawa masu fada a ji saboda yanda suka yiwa mata.