Yajin Aikin ASUU: Buhari Ya Gana Da Masu Ruwa Da Tsaki

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaba da wasu zababbun mambobin kwamitin shugabannin gudanarwar jami’o’in tarayya kan batun yajin aikin kugniyar malaman ASUU.

Shugaban ya yi alkawarin ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, domin kawo karshen yajin aikin da malaman jami’o’i suka dade suna yi a karkashin kungiyar malaman jami’o’in kasar ta ASUU.

Mai taimaka wa shugaban Najeriya kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Juma’a.

Farfesa Nimi Briggs, shi ne ya jagoranci zaman wanda ya ce sun yi da nufin ganawa da shugaban kasa a matsayinsa na shugaba kuma babban kwamandan sojin kasar, a matsayin uban kasa, kuma a matsayin mai ziyartar jami’o’in gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa, duk da rashin jin dadin da yajin aikin na sama da wata bakwai ya haddasa, “makomar jami’o’in kasar na da armashi,” har ya bada misali da jami’ar Ibadan da ta shiga jerin sunayen jami’o’i 1,000 masu kyau a duniya, wani ci gaba da aka gani a karon farko.

Farfesa Briggs ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa amincewar da ta yi da wasu bukatun malaman da ke yajin aiki, ciki har da bukatar karin albashin bai daya na kashi 23.5 cikin 100, da kuma karin albashin Farfesoshi da kashi 35 cikin 100. Ko da yake, Briggs ya nemi a dan kara albashin la’akari da yayanin tattalin arzikin kasar.

Shugabannin gudanarwar jami’o’in sun kuma bukaci a sake duba matsayin gwamnati na “idan ba ka yi aiki ba babu albashi,” yayin da suka yi alkawarin cewa malamai za su yi aiki don cike gibin da aka samu tsawon lokacin yajin aikin da zarar an cimma matsaya, an kuma bude makarantu.

Karamin ministan Ilimi, Goodluck Nana Opiah, yace duk abubuwan da gwamnatin tarayya ta cimma matsaya a kansu don ganin an kawo karshen yajin aikin ne, amma kungiyar ASUU ta ki.