Al'amarin ya jefa daruruwan mutanen jihar dake anfani da kafofin labaran cikin wani hali na rashin samun bayanan komi daga kafofin labarun kamar yadda suka saba.
Sadiq Muhammad Aliyu shugaban kungiyar RATAWU a jihar yace abubuwa sun yi zafi. Yace na farko akwai yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin jihar akan wasu alawus alawus tun shekarar 2012 suna ta fama da gwamnati ta amince da abun da shugaban kasa ya riga ya sawa hannu. Sauran jihohin kasar sun kuma amince da karin da aka yi masu.
Lokuta sau da yawa sun zauna da shugaban ma'aikatan gwamnati da sauran manyan. Sun kwashi shekaru biyu suna tattaunawa akan abu daya. Amma har yanzu babu wani alamar cewa gwamnati zata aiwatar da yarjejeniyar.
Shugaban RATAWU na arewa maso tsakiya Ahmed Mukhtari Kontagora ya kira gwamnan jihar Neja da sunan Allah ya taimaka ya biya albashin da alawus din. Ya rokeshi da sunan Allah ya taimaka ya biyawa ma'aikatan bukatunsu.
Tuni dai al'ummar jihar suka fara kokawa sakamakon shirun da suka ji daga kafofin labarai tun daga ranar Litinin din nan.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5