Hanya daya da gwamnati za ta bi wajen kawo gyara ga masu shiga masana’antar Kannywood ta bayan katanga ba tare da an tantancesu daga jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar ba, ita ce sai gwamnati ta kafa matakai masu dorewa don magance matsalolin da ke yi wa masana’antar barazana.
A lokacin da Malama Hasali ke zantawa da wakiliyar Dandalin VOA a Kano, tace lallai a kafa kwamitin wata daya kacal, domin tabbatar da an magance matsalar shiga masana’antar ba bisa ka'ida ba, ta haka ne za a iya magane matsalar, haka kuma dole sai ana bibiyar al’amarin akai-akai.
Ta ci gaba da cewa harkar fim a lokacin baya da wannan lokacin ya banbamta. Yanzu an samu ci gaba na kayayyakin aiki da sauran yadda ake gudanar da fina-finai, hada da wadanda suke shirya- fina-finai, sai dai yana tattare da akasi na yadda ake daukar masu gudanar da ita.
Ta ce a yanzu tsarin shirya fin-finai yana da 'yar matsala, duk wanda yake so ya shiga harkar fim din, ba kafar kowa ma yana da ‘yancin shiga masana’antar wanda hakan ya haifar da rashin da’a da samar da abin da ake bukata.
A don haka ne a yanzu ake yunkuri kawo gyara da tsaftace masana’antar , inda gwamnati ta kwafa wani kwamiti da ya hada da wakilai na masu kamara da rubuta fina-finai da sauran sassan na harkar fim domin a tsaftace harkar.
Wannan kwamiti dai zai dauki wata guda inda za’a lalubo hanyoyin da za’a tantantace sabbin jarumai da suke harkar fina-finai, shin sun bi ka’idoji ko akasin haka.
Your browser doesn’t support HTML5