Yadda ‘Yan bindiga Suka Sace Daliban Jami'a A Kaduna

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan bindiga.

Shaidu sun ce maharan sun yi ta harbi a sama kafin daga bisani su kwashe daliban su kutsa da su cikin daji.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari cikin wata jami’a mai zaman kanta a jihar Kaduna a ke arewacin Najeriya, inda suka yi awon gaba da daliban da ba a tantance yawansu ba.

Maharan sun kai farmaki ne a Jami’ar Greenfield a karamar hukumar Chikun da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a daren Talata. Hukumomin jihar sun tabbatar da aukuwar wannan lamari.

Bincike ya nuna cewa shekara uku da suka gabata aka bude jami’ar ta Greenfield.

Shaidu sun ce maharan sun yi ta harbi a sama kafin daga bisani su kwashe daliban su kutsa da su cikin daji.

Wannan hari na zuwa ne sama da wata guda bayan da ‘yan bindiga suka sace daliban makarantar horar da ilimin albarkatun daji da ke Afaka a jihar ta Kaduna.

Lokacin da aka sako daliban Jengebe da aka sace a jihar Zamfara

Bayanai sun yi nuni da cewa, har yanzu akwai wasu daga cikin daliban 39 da ba a kubutar da su ba.

A baya, Gwamna Malam Nasir El Rufai, ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kudin fansa ba, kuma ba ta da shirin yin sulhu da ‘yan bindigar kamar yadda wasu jihohi ke yi.

Matsalar garkuwa da mutane, ta zama ruwan dare a arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya sa aka yi ta rufe makarantu.

A makon da ya gabata, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce an rufe makarantu sama da 600 tsakanin watan Disambar bara zuwa watan Maris saboda hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa makarantu.