Rahotanni daga birnin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, na nuni da cewa masu sayar da burodi sun kara farashinsa a birnin.
Masu sana’ar sayar da burodi sun ce karin farashin na da nasaba da karancin alkama da ake fuskanta tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
“Ita alkama ba a Najeriya ake noma ta ba. Fadan Ukraine da Rasha, shi ne ya kawo matsala.” In ji Alhaji Bukar Mustapha, shugaban masu gidajen gasa burodi a Maiduguri.
Rasha na gaba-gaba a jerin kasashen duniya da ke noma alkama, kuma yanzu haka tana fama da takunkumai da aka kakaba mata saboda mamayar da ta yi wa Ukraine.
Tuni dai mazauna birnin na Maiduguri suka fara bayyana kokensu kan wannan al’amari
“Wannan tsadar rayuwa da muke ciki sai dai mu yi addu’ar Allah ya yaye mana. Gaskiya babu wani fita da muke yi a wannan sana’a.” In ji Musa mai shayi.
Burodi na daya daga cikin nau’ukan abinci da ake yawan amfani da shi a sassan duniya.
A shekarun baya, ya kasance wani abu da marasa karfi kan iya dogaro da shi a matsayin abin karin kumallo.
Amma a baya-bayan nan, farashin na kara hauhawa, lamarin da ke kara nesanta shi da talakawa.
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:
Your browser doesn’t support HTML5