Hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta jagoranci wani zama da matasa masu yin TikTok a jihar.
Zaman kokari ne na ganin an kwadaitar da masu yin TikTok wajen yada ayyukan alkairi maimakon na badala a cewar hukumar.
“Hukumar Hisba a matsayinta na uwa na uba, muka ga cewa, bai kamata mu zura ido muna ganin abubuwa suna tabarbarewa ba, don haka muka gayyace ku a matsayinku na matasa.
“Wacce irin gudunmawa za ku ba wa hukumar Hisbah, domin shawo kan matsaloli da ake samu a TikTok.” In ji Shugaban Hisba, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Jama’a da dama kan zargin ‘yan TikTok da bata tarbiyyar matasa duba da irin hotunan bidiyo da suke yadawa a shafin na sada zumunta.
A watan Satumbar 2023 kamfanin na TikTok ya sanar da cewa masu amfani da manhajar sun kai biliyan a daya a duniya.
Sheikh Daurawa da ya jagaoranci zaman ya jaddada cewa burin Hisbah shi ne “umarni da aikin alheri da hani da mummuna.”
Hisbah ce ta gayyaci masu amfanin da manhajar ta TikTok, ko da yake wasunsu ba su halarta ba, bayan da aka yi ta rade-radin cewa dabara ce ta a damke su, zargin da Hisbah ta musanta tun kafin taron.
"Masu tsoro dai ga shi nan babu abin da ya faru, alhamdulillah." In ji wata 'yar TikTok a zantawarta da Freedom Radio.
Da yawa daga cikin wadanda suka halarci taron sun yaba da gayyatar da hukumar ta Hisbah ta yi musu, inda suka yi alkawarin kyautata yadda suke yada al'amuransu a shafin na TikTok.
Ga alkawuran da hukumar ta Hisba ta yi wa ‘yan TikTok:
- Masu bukatar yin aure, za a musu
- Masu bukatar koma wa makaranta za a dauki nauyinsu
- Masu bukatar jari don yin sana’a za a ba su
- Wadanda suke fama da wata larura ta rashin lafiya za a taimaka musu wajen nema musu magana.