‘Yan ta’adda shida ne rundunar da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta ta STF ta halaka yayin da jami’an ‘yan sanda uku suka rasa ransu.
Lamarin ya faru ne a wani artabu da bata garin a yankin Bwai dake karamar hukumar Mangu a jihar.
Kakakin rundunar tsaro ta Special Task Force (STF) a jihar, Manjo Ishaku Takwa ya ce, rundunar ta sami kiran neman agaji ne daga jami’an ‘yan sandan na musamman dake binciken masu laifi, a lokacin da suka je bincike ‘yan bindigar suka auka musu suka kashe ‘jami’an ‘yan sanda uku suka arce da makamansu.
“Wadannan ‘yan sanda masu farin kaya sun je ne su yi bincikensu abin da ya kai ga arangama har aka kashe mutum uku a cikinsu.” In ji Manjo Takwa.
Manjo Takwa ya ce jami’an sojoji da DPO a yankin sun bi sawun ‘yan ta’addan inda suka tarar da su, suka kuma halaka mutum shida a cikinsu tare da kwato makaman da suka kwace a hannun ‘yan sandan da suka kashe.
Hakimin yankin na Bwai, Da Gabriel Gusat ya ce kamata ya yi a girke musu rundunar tsaro a yankin, saboda a kwanakin baya ma ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda uku a wurin.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5