Tsananin sanyi a garin Jos da ke jihar Pilato ya takura jama'a, yadda da dama suka kasance a cikin daki suka kasa fita gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Tun ranar Laraba, daya ga watan Janairun 2020 ne matsanancin sanyi ya sauko a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.
Wasu mazauna garin Jos da dama, sun ce an jima rabon da a ga irin wannan sanyi.
Hukumar nazarin yanayi a Najeriya, ta yi hasasen yanayi mai sanyi a wasu sassan kasar, ciki har da Kano, Kaduna da katsina a Arewacin Najeriya.
Da yawa daga cikin jama'a sun ce sanyi bana ya fi na bara, kuma dole suke lullube kansu, ko da a cikin gidajensu.
Hukumomi kuma sun nem i da a yi taka-tsantsan domin akwai cututtuka da wannan sanyi zai iya haifarwa.
Amma ga wasu 'yan kasuwa, lokacin samun riba ne, domin suna samun kudi daga kayan sanyi da suke sayarwa a wannan lokaci.
Ga cikakken rahoto cikin sauti daga jihar Filato.
Your browser doesn’t support HTML5