A hirar ta da Muryar Amurka yayin ziyarar jaje da ta kaiwa iyayen Hanifa Abubakar, ‘yar shekaru biyar da ake zargin Abudulmalik Tanko ya yi garkuwa da ita, daga nan ya kashe ta, ta ce, kamata ya yi a rika gaggawar tuhuma da kuma hukumta dukan wadanda ake kamawa da irin wannan laifin.
Bisa ga cewarta, tara irin wadannan mutanen a gidajen yari ba alheri ba ne ga al’umma, domin jama’a za su ga ba a komi. A maimakon haka, za a ci gaba da samun masu aikata irin wadannan laifuka kasancewa ba a dauki matakin da zai iya zama ishara ga wadansu ba.
Ku Duba Wannan Ma Babu Wanda Ya Illata Jikin Hanifa-AbdulmalikHajiya Halima ta bayyana takaicin ganin yadda ake kama masu yiwa kananan yara fyade ko kuma cin zarafin kananan yara da aka sani suna zaune tsakanin al’umma, da wadansu lokuta akan kama su a kaisu ofishin ‘yan sanda. ‘Yan sanda kuma sun san da zamansu, kuma sun amsa laifukan, amma a karshe ba a sake jin abinda ya biyo baya.
Ta yi misali da yadda wani tsoho ya fada da bakinshi cewa, ya yi wa wata karamar yarinya ‘yar shekaru uku fyade. Tace jin iri-irin wadannan labaran a matsayin uwa tilas ne hankali ya tashi.
Mai dakin tsohon gwamnan jihar Kanon tace, ya kamata abinda ya faru da Hanifa ya sa hukumomi su farga, su dauki matakin a kan masu garkuwa da mutane da kuma yi wa kananan yara fyade ko cin zarafin su ta kowacce fuska. Tace tilas ne hukumomi su rika tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Bisa ga cewarta, daukar matakin gaggawa kuma tsats-tsaura zai sa duk mai tunanin aikata irin wannan laifin sake tunani.
Hajiya Halima tace, a matsayinsu na iyaye, ba zasu lamunci ci gaba da cin zarafi da kuma kashe kananan yara ba sabili da sakacin al’umma. Ta ce ba ta san Hanifa ko kuma iyayenta ba, amma duk mace ta san dadin da, ta kuma san zafin rasa shi. Sabili da haka, take kira ga hukumomi su dauki matakin kare rayukan kananan yara.
Hanifa Abubakar ‘yar shekaru biyar da haihuwa, kuma ‘ya daya tilo ga mahaifanta Abubakar Abdulsalam da Murja Suleiman, ta rasa ranta ne bayan da aka yi zargin cewa, mai makarantar da ake kira Nobel Kids dake Kwanar Dakata, Karamar Hukumar Nassarawa, jihar Kano, ya yi garkuwa da ita, daga nan ya kashe ta da maganin bera.
Ku Duba Wannan Ma Hanifa: Abinda Mai Yiwuwa Ba Ku Sani Ba Daga Bakin Mahaifiyarta