Bayan wata ziyara da wasu gwamnonin Najeriya suka kai a gidan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake jinya a ranar Laraba a London, bayanai masu dadi kara na kara fitowa kan halin da shugaban ke ciki.
Gwamnoni bakwai daga shiyyoyin Najeriya shida sun samu jagorancin gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin kasar inda suka kai wa Buhari ziyara.
Gwamnonin sun hada da Dave Umahi na Ebonyi da Abdullahi Umaru Ganduje na Kano da Kashim Shettima na Borno da Samuel Ortom na Benue.
Sauran sun hada da Udom Emmanuel na Akwa Ibom da Abiola Ajimobi na jihar Oyo.
A baya an yi ta rade-radin cewa shugaba Buhari na cikin mawuyacin hali, saboda rashin fitowarsa baina jama’a tun da ya tafi kasar ta Birtaniya neman magani kan cutar da har yanzu ba a bayyana ba.
Wannan ziyara na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata makamanciyar ziyara da gwamnonin jihar Imo Rochas Okorocha da Nasiru El Rufa’i na Kaduna da Yahaya Bello na Kogi da Tanko al Makura na Nasarawa suka kai mai a karshen makon da ya gabata.
Domin jin bayanan da wasu daga cikin gwamnonin suka yi kan ziyarar ta jiya Laraba saurari hirar da wakilinmu Nasiru Adamu El Hikaya ya yi da wasu daga cikinsu:
Your browser doesn’t support HTML5