Wannan lamari ya auku a lokacin jawaban sallar Idin karamar sallah a masallacin anguwar 'yan majalisar dokokin Najeriya da ke Apo Abuja.
Masallacin dai wanda tun a tarihi jama'a su ka tara kudi su ka gina, ya na daf da gidan nan na kakakin majalisar wakilai da gyaran gidan kan kimanin naira miliyan 600 ya haddasa tsige kakakin majalisa Patricia Eteh, har Allah ya karbi rayuwar dan majalisa Aminu Safana.
Lokacin da Imam Ibrahim Auwal Usama ke jawabi ya nuna rashin tabuka abun kirki na gwamnatin Buhari ga al'ummar arewa da karfafa cewa tamkar 'yan kudu ne su ke cin gajiyar gwamnatin alhali shugaban dan tsakiyar arewa ne.
Imam Usama ya ba da misali da rashin kammala gyaran hanyar Abuja zuwa Kano da tabarbarewar tsaro.
Wannan ya sa dan siyasar jihar Zamfara tsohon Sanata Sa'idu Dansadau ya kasa jurewa ya zo ya karbe na'urar magana ya ce a yi wa gwamnatin shugaba Buhari adalci don ta ba da tallafi ko basuka ga jama'a.
Karin bayani akan: Allah, jihar Zamfara, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Hakan ya sa mutane fusata da bukatar ya rufe masu baki, inda shi kuma ya ce irin wannan bijirewa hatta Annabawa an yi masu irin ta.
Dansadau wanda duk da dan siyasa ne, kan karantar da littafin Ahlari a karamin masallacin Jumma'a na anguwar da ke Zone A.
Imam Usama ya karbi abin magana inda ya jagoranci kada kuri'ar dawowa daga rakiyar gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari.
Bayan da ya kammala sallar Idi a a fadarsa, Buhari ya fadawa manema labarai cewa, ya kamata jama'ar Najeriya su nuna fahimta kan matsalolin da ke addabar kasar, musamman na tsaro.
Buhari ya kara da cewa, ya kamata jama'a su kara hakuri lura da irin taruka da matakai da gwamnatinsa ke dauka wajen shawo kan matsalolin kasar.
Anguwar Apo dai ta kasance da tsoffin 'yan majalisa da sabbi da kuma masu hannu da shuni tun sanadiyyar neman tazarcen shugaba Obasanjo gabanin zaben 2007 ya sayarwa 'yan majalisa gidajen tamkar kyauta don neman a mara ma sa baya. Lokacin Nasiru El Rufai ke ministan Abuja.
Saurari cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5