Hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH da kungiyoyin kare hakkin mata a Jamhuriyar Nijar, sun shirya taron mahawara akan matsalar fyade a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula da kuma irin gudunmowar da mata ke iya bayarwa wajen magance matsalolin tsaro a kasar.
Gomman jami’an tsaro mata ne aka tattara a wurin wannan mahawara da nufin nazarin hanyoyin da za a bullo wa matsalar fyade a Jamhuriyar Nijar, bayan la’akari da yadda abin ke kokarin samun gindin zama a yankunan da ke fama da aika-aikar ‘yan bindiga.
Shugabar kungiyar yaki da dabi’ar muzgunawa mata da yara ONG SOS FEVF Mme Ahmed Mariama Moussa, na daga cikin shika shikan wannan haduwa.
Bayanai sun yi nuni da cewa wasu mata kan taimaka wa ‘yan ta’adda wajen shirya aika-aikar da suke tafkawa dalili kenan wannan taro a wani bangarensa ya tattauna wannan al’amari.
Hukumar kare hakkin dan adam ta kasa wato CNDH ce ta shirya wannan taron mahawara domin ganar da jami’an tsaro mata rawar da ya kamata su taka a kokarin magance matsalolin tsaro.
Dabi’ar fyade da akasari ake alakantawa da ta’ammali da miyagun kwayoyi ko wani abin da ke da nasaba da gushewar hankali, na daga cikin manyan laifukan da kasashen duniya suka yi tanadin hukunci mai tsanani akansu.
Sai dai duk da haka, abin na neman zama tamkar ana magani kai ya na kaba dalili kenan da ya sa hukumomi da kungiyoyi ke kara matsa kaimi wajen ayyukan fadakarwa a game da illlolin da abin ke haifarwa zamantakewar jama’a.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumoni Barma daga birnin Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5