An fara wani taron koli na (FOCAC) tsakanin shugabanin kasashen Afirka da China domin bitar huldar da ke tsakanin bangarorin biyu, musamman ta hanyar da za su kara kyautata dangantar da ke tsakaninsu.
Taron kamar yadda bayanai ke nunawa, zai yi dubi kan yadda China za ta taimaka wajen raya fannin sufuri a nahiyar da sauran fannonin ababan more rayuwa.
Daga cikin shugabannin da ke halarta taron, akwai shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu, Abdel Fatah al Sisi na Masar, Edgar Lungu na Zambia da kuma Ali Bongo na Gabon.
An jima ana samun rarrabuwar kawuna a tsakanin masu fashin baki, kan yadda suke kallon wannan dagantaka tsakanin kasashen na nahiyar ta Afirka da China.
Yayin da wasu ke kallon huldar a matsayin wacce za ta amfani kasashen na Afirka, wasu kuwa na ganin akwai bukatar nahiyar ta yi taka-tsatsan, kada ta fada cikin kangin basussuka.
China ta jima tana musanta wannan ikrari, ta hanyar yin watsi da zargin da wasu ke yi na cewa, tana kokari ne ta dora basussuka akan kasashen na Afirka.
Ta kuma kare kanta kan sukar da wasu ke yi na cewa, kokari take yi ta kwashe albarkatun kasashen na nahiyar Afirka.
Bayanai daga wani binciken hadin gwiwa da bangarorin biyu suka yi, wanda Jami’ar Johns Hopkins da ke Amurka ta taskance, sun nuna cewa a tsakanin 2006 zuwa 2016, China ta bai wa Afirka bashin dalar Amurka biliyan 125.
Masana tattalin arziki irinsu Dr. Soli Abdullahi da ke Jamhuriyar, na ganin yunkurin da China ke yi na mannewa nahiyar Afirka, kokari na tsame nahiyar daga kangin kasashen yammaci.
Saurari cikakkiyar hirar ta Dr. Abdullahi da wakilinmu Sule Mumuni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5