Bangaren Majalisar Dokokin Najeriya, wani bangaren ne shima da ke shirin cika shekara guda da kafuwa, wato a jamhuriyar ta takwas.
WASHINGTON D.C. —
Wannan Majalisa, ita ma ta yi fadi tashi daga farkon lokacin da aka kafa ta zuwa yanzu.
Majalisar ta dokokin Najeriya, kama daga ta dattawa da ta wakilai duk sun sha fama da matsalar shugabanci.
To amma masu lura da al’amura sukan maida hankali ne kan irin rawar da majalisar ta taka wajen sauya rayuwar ‘yan Najeriya.
Musamman ta fannin abin da ya shafi samar da doka ko amincewa da wani kudiri wanda zai yi tasiri na kai-tsaye ga rayuwar talaka.
Wakiliyar Muryar Amurka, Medina Dauda ta yi mana dubi kan yadda majalisar dattawa da ta wakilai suka kaya yayin da suma su ke shirin cika shekara guda:
Your browser doesn’t support HTML5