Sallar ta bana na zuwa ne a wani lokacin da ake cikin yanayin fatara da talauci a mafi yawancin kasashen duniya, lamarin da ya sa wasu Kiristoci takaita hidimomin sallar dai-dai ruwa dai-dai tsaki.
Kamar yadda aka saba a kowace shekara, idan wannan lokaci ya zagayo a wannan karon ma kristoci a nan Nijar kamar sauran takwarorinsu na sassan duniya za su hallara majami’u domin addu’oin neman ceto a albarkacin bikin na Easter ko kuma Pacques kamar yadda wani limamin Churchin Assemlee des Dieux dake unguwar Zarya Maradi Reveran Pasteur Benjamin Bernard Evodavi ya bayyana.
A cewar Evodavi, Yesu ya zo ne saboda ya biya hukuncin zunubi, bayan kwana 3 sai ya tashi.
Madame Kerry Habibi wata uwar iyali a Damagaram ta ce bikin na Easter, wani lokaci ne na shirya liyafar cin abinci da zuwa ziyarar ‘yan uwa har ma da ba da kyaututuka to sai dai a bana wannan biki ya zagayo a wani lokacin da ake cikin yanayin talauci.
Wannan ya sa hadimai a majami’u irinsu Adamou Maidaji na Churchin EERN dake unguwar bayan ruwa birnin Yamai ankarar da attajirai mahimmanci taimakon masu karamin karfi.
Tunatarwa akan halaye da dabi’un da aka hori Kiristoci su yi koyi da su na kan gaban abubuwan da limamin addinin Kirista ke maida hankali akansu a irin wannan lokaci.
A majami’ar EERN shiyyar Yamai ta 5 Reveran Pasteur Habibou ya yi nasiha ga daukacin al’umar Nijar.
Ya ce ko wani mutum ya nemi ceto. Tsadar rayuwar na yanzu na neman addu'a.
A bana ranar Lahadi 17 ga watan Afrilu ita ce ke daidai da ranar zagayowar tashin Annabi Isa Alaihi Salam wace Kiristoci za su yi amfani da ita domin sujadar neman ceto tare da yi wa mahalicci godiya akan dukkan alhairan da ya saukar y
A kuma yammacin wannan Juma’a da suke kira Juma’a mai tsarki ko kuma Vendredi Saint za su hallara majami’u da nufin tunawa da ranar mutuwar Yesu almasihu,.
Albarkacin bikin na Eeaster ko Pacque hukumomi sun ayyana ranar Litinin 18 ga watan nan Afrilu a matsayin ranar hutu a ko ina a fadin Nijar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5