Yadda Kasuwar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Ke Wakana

A yayinda ake cigaba da hada hadar saye da sayar da ‘yan wasan kwallon Kafa na duniya a watan janirun shekarar 2018, Kungiyoyi da dama musamman a nahiyar turai sun dukufa wajan ganin sun kammala cinikayyar ‘yan wasa kafin arufe kasuwar a karshen watan.

A karon farko Alexsi Sanchez, ya Sanya rigar kungiyar Manchester united mai lamba 7 bayan dan wasan ya kammala gwajin lafiyarsa a kungiyar, bayan ya rattaba hanu kan yarjejeniyar kwantiragin shekaru hudu da rabi inda zai zamo Dan wasan da yafi kowane dan wasan Firimiya lig daukar albashi kimanin fam dubu £450 a sati.

Nan da wasu a awoyi ake sa ran Manchester united, zata bada sanarwar kammala daukar dan wasan a hukunce. An bayyana sunan Javi Gracia a matsayin sabon Kocin kungiyar kwallon Kafa ta Watford, inda ya maye gurbin Marco Silva, wadda aka sallame shi a watan Nuwambar shekarar 2017 da ta wuce.

Gracia dan kasar Spain 47 ya karbi kwantiragin watanni 18 a kungiyar Watford, Kuma shine manaja na goma a kungiyar daga 2012, Gracia ya yi aiki da kungiyar malaga ta kasar Spain a matsayin koci. Watford a yanzu tana matsayi na 10 a teburin Firimiya lig da maki 26 a wasanni 23 da ta buga.

Kocin zai fara kama aiki na atisaye a Yau Litinin inda zai fara wasansa na farko a kungiyar ranar Asabar a gasar FA Cup zagaye na hudu tsakaninsu da Southampto. Arturo Vidal ya ce ba wani batun barin kungiyar ta Bayern Munich, a wannan watan janairu.

A yanzu kan ya maida hankalinsa ne wajan lashe kofin zakarun nahiyar turai, Kungiyar Chelsea ta kasar Ingila ta nuna sha'awarta ta ganin ta dauko dan wasan.

Shugaban kungiyar Arsenal yana kasar Jamus domin ganin an cimma yarjejeniya kan batun sayen dan wasan gaba na Borussia Dortmund Emerick Aubameyang, domin ya maye gurbin Alexsi Sanchez wanda ya koma Manchester united da taka leda.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Kasuwar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Ke Wakana