Gwamantin Amurka na yunkurin gabatar da wani shiri da zai kawa masu shirya fina-finai na masana'antar Kannywood, don su koyi yadda ake hada fim na "documentary" domin fito da tarihin Kano, sarakunan kasar Hausa, da wasu muhimman mutane da suka taka muhimmiyar rawa da sauransu.
Hukumar tace fina-finai na fito da hanyoyin da za su bunkasa sana’a domin samar da ayyukan yi ga matasa.
Ismaila Na’abba Afakallah, ya kara da cewa shigowar gwamantin Amurka zai taimaka wajen fito da tarihin kasar Hausa, ga duniya da ma matasa masu tasowa baya ga fito da wasu muhimman mutane da suka taka rawa a kasar Hausa, kama daga kan sarakai masu ilimi da ma wadanda suka ba da wata bajinta ga alummarta.
Yana daga cikin kundin masana'antar, samar da sana’a cikin ingantaccen yanayi domin ci gaban kasar, har illar yau ya ce gwamantin Amurka ce ta nemi masana'antar domin su ga yadda za’a samar da yanayi ta yadda take samawa matasa ayyukan yi.
A hannu guda kuwa daya daga cikin jigo na masana'antar Kannywood Hafizu Bello ya ce masana'antar Kannywood ba su san kasuwar shirya fim na documentary ba, wanda wannan na daya daga cikin dalilai da ya sa suke koma baya, domin kuwa masana'antar kannywood ba ta shirya film festival wato baje kolin fina-finai.
Hafizu Bello, ya ce rashin wakilci a masana'antar ne ya haifar da rashin shiga ire-iren wadannan shirye-shirye na baje kolin fina-finai, da ma shirya fim irin na documentary, domin mafi akasari 'yan Kannywood kan nisanta kansu da Nollywood.
Yana ganin cewar akan samu karanci ilimin na shiga ire-iren shirye-shiryen, don shiga sahun duniya wajen shirya fina-finai.
Your browser doesn’t support HTML5