Yadda Jami'an Tsaro Suka Kubutar Da Mutum 77 Da Aka Tsare A Dakin Wata Mujami'a A Jihar Ondo

  • Hasan Tambuwal

Jami'an 'yan sanda yayin da suke tsaye a kusa da sakatariyar gwamnatin tarayya a Abuja. (Mun yi amfani da wannan hoto ne don nuna misali)

Hukumomin sun ce sun kai samame Cocin cene  bayan da wasu iyaye suka kai korafi wajen hukuma.

Hukumomin tsaro a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya, sun kama Pastocin Mujami’ar Whole Bible Believers Church, bayan da aka kubutar da mutum 77 da ake zargin garkuwa aka yi da su, a wani daki da ke karkashin ginin Cocin a karshen makon nan.

Rahotanni sun ce, wasu daga cikin mutanen sun kai tsawo wata shida, a tsare a cocin.

Wata matashiya ta fadawa jaridar Punch da ake wallafa a Najeriya cewa, “na yanke shawarar shiga Cocin ce saboda iyayena suna janye ni daga bin dokokin Allah, alhali ina so na shiga Aljanna.”

Hukumomin sun ce sun kai samame Cocin cene bayan da wasu iyaye suka kai korafi wajen hukuma.

‘Yan sanda sun ce sun kama pasto da wasu mambobin Cocin.

Saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal daga Ibadan:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Jami'an Tsaro Suka Kubutar Da Mutum 77 Da Aka Boye A Dakin Wata Mujami'a A Jihar Ondo - 3'02"