Matsalar shaye shaye a tsakanin matasa ta zama tamkar wutar daji, kuma wannan mummunar dabi'a na ci gaba da yaduwa har zuwa wasu magidanta musamman mata da 'yan mata.
Ta dalilin haka ne dandalinvoa ya sami zantawa da malama Maryam Muhammed kwararriya kuma jagorar kungiyar Youth Awareness Against Drugs Abuse Initiaves wadda ke fadakar wa akan illar shaye shaye inda tayi mana bayani akan wasu dalilai da ke jefa wasu matasa cikin irin wannan hali, da kuma illar sa.
Kayan sa maye ka iya kasancewa masu nau'in magunguna ko kuma abinda matasan suka kirkira da kansu, Malamar ta bayyana cewar duk iya shekarun da mai bincike zai yi yana karatun wannan matsala, kusan ko wane lokaci sai ya ci karo da wani abin da zai daure mai kai.
Rashin aikin yi, da bakin ciki ko rashin masoya ko daya daga cikin iyaye kan jefa wasu cikin wannan hali, baya ga haka a cewar malama Maryam, gata ma nasa wasu matasa cikin wannan hali na shaye shaye. A wani lokaci samari kan koya wa 'yan mata, kokuma bakin cikin da mai gida kan sa ma matarsa kan jefa ta cikin wannan hali.
Dabi'ar wanda ke wannan harka na canzawa, iyaye su lura da duk wani canjin halin yara su kama daga yawan bacci da kuma karya, yawan yawo da leda ko tsumma, ko kuma kwalabe a dakin yaran, da kuma rashin kunya kai harma yawan amfani da turare mai karfi da sace sace da yawan yawo.
saurari cikakkiyar hirar