KANO, NIGERIA - Hukumomi da kungiyoyin gwagwarmayar ‘yancin yara na ciki da wajen Najeriya sun himmatu wajen dakile ta'adar cin zarafin yara, musamman fyade ga yara mata, ta hanyar tsayin daka domin tabbatar da hukunci ga masu laifi.
Sai dai a hannu guda kuma, yadda galibin iyayen yaran da irin wannan abu ya faru da su suna yawan janye bukatun neman hakkin ‘ya’yan su avgaban kotu ko ofisoahin ‘yan sanda abinda ya zamana abin damuwa ga masu kokarin kwato masu hakki ko ‘yanci.
Barr Amina Umar ta reshen Jihar Jigawa na ofishin lauyoyin tarayya masu bada agajin kariya ga ‘yan kasa masu rauni ta fayyace wasu daga dalilan haka. Ta ce dalilan suna da yawa amma akwai guda biyu na musamman dake sa iyayen janye kararsu daga kotu.
Barrista Amina ta ce na farko shine tafiyar hawainiya da ita kanta bincike da shari’a suke yi, akwai kuma tsada Akan tafiyar da harkar irin wannan shari’a.
Bisa ga cewar ta, akwai kuma larurar jeka ka dawo na tilasta raunanan talakawa hakura da neman hakkin ‘ya’yan su, amma Barista Amina ta ce janye karar, hakan ba ita ce mafita ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5