Wannan ya biyo bayan mummunar barakar da ta dabaibaye kungiyoyin 'yan ta'addan ne saboda wasu matsaloli daban-daban.
Wani masanin tsaro dan asalin yankin tafkin Chadin Dr. Abubakar Mohammed Sani ya shaida wa Muryar Amurka cewa biyo bayan luguden wuta da sojojin kawance na kasashen yankin tafkin Chadin suke ta yi wa 'yan ta'addan, ya sa mayansu da dama suna ta mika wuya.
Yayin da wasu daga cikinsu kuma ke da ra'ayin ayi sulhu da gwamnati, wannan ra'ayi ne kuma ya harzuka sauran masu tsatsauran ra'ayi daga cikinsu al'amarin da ya kai ga uwar kungiyar ta yanke tare da zartas masu da hukuncin kisa.
Mai bincike kan ta'addanci, Dr. Kabiru Adamu ya shaida wa VOA cewa, akwai yiwuwar nan da 'yan kwanaki a samu karin hare-hare na ta'addanci da ma kunar bakin wake, kwatankwacin yadda ya faru a yankin Sahel.
Sai dai a daya bangaren kuma, rundunar tafkin Chadin ta sha alwashin ci gaba da kaddamar da hare-hare akan yan ta'addan har sai ta kakkabe su.
In za a iya tunawa a 'yan watannin baya, rundunar ta MNJTF ta samu nasarar halaka wasu manyan kwamandojin I.S. din a tafkin Chadin.
Your browser doesn’t support HTML5