WASHINGTON, DC —
Da alamun dai Sallar layya ta bana, ta zo ne a wani yanayi na rashin kudi a hannun jama'a, domin kuwa farashin raguna yayi tsanani, kamar yadda wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Abdul'aziz ya tarar a kasuwar dabbobi ta Yola da Jalingo.
Sai dai lokacin da kasuwar dillalan raguna ke kara buduwa a yanzu, su kuwa talakawa suna nuna damuwa ne akan tsadar raguna a yanzu.
Su kuwa hukumomin tsaro, a halin yanzu, suna cikin shirin tabbatar da anyi shagulgulan babbar Sallah cikin kwanciyar hankali.
Suleiman Baba, kakakin rundunan tsaron farin kaya, a hirar su da wakilin mu, ya bayyana irin matakan da aka dauka.
A saurari cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5