Yadda Daya Daga Cikin Daliban Da Aka Sace a Katsina Ya Kubuta

Makarantar da aka dauke dalibai a jihar katsina

‘Yan bindiga sun tasa keyar wasu dalibai cikin daji da ke jihar Katsina a Arewacin Najeriya. Usman Aminu Mali, ya yi ta tunanin ko shi da sauran daruruwan daliban da aka sato su za su iya kai labari?

Matashin dan shekara 18 da haihuwa. ya ce ya ji daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su yana tambaya, a cikin kiran waya, “Yallabai, za mu sake su ne ko mu kashe su?” Ku ci gaba da aiki. Hakan ya na samu kwanciyar hankali, Usaman ya ci gaba da tafiya yana addu’a.

An kubutar da shi a ranar Lahadi da safe, sa’o’i 30 bayan da ‘yan bindiga akan babura suka kai hari makarantar kwana ta maza ta GSS Kankara a ranar Juma’a da daddare, suka yi garkuwa da daruruwan dalibai kana suka tasa keyar su dajin Zango.

Har zuwa ranar Talata ba’a ga kusan dalibai 300 ba, yayin da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi ikirarin sune suka yi garkuwa da su.

Addu’a da rashin lafiya, sun taimakawa Usman wajen samun kubuta kamar yadda ya bayyana, yayin da yake zantawa da Muryar Amurka akan abun da ya faru. Saboda dalili na tsananin rashin lafiya, yasa aka bar shi a baya – hakan kuma ya taimaka mai.

Bayan da ‘yan bindigar suka shiga cikin makarantar sai suka tara dalibai, “mun yi tafiya tsawon daren a cikin daji, da yawa daga cikinmu sun rasa takalmansu saboda sun bata, yayin da suke ficewa daga makarantar. Ina tafiya ba takalmi, ina ta taka kaya.”

Ranar Asabar, Usama ya ce ya ji karar jirgin sama yana shawagi, hakan ya sa ‘yan bindigar suka tsaya. Bayan da jirgin ya wuce, sai aka umurci daya daga cikin daliban da ya kirga mu.

“Ya kidaya mutum 520,” in ji Usman. Sai suka tambaye mu waye zai iya ciyar da dukanku ku 520? Sun ce mun fi zama musu matsala sama da ‘yan matan Chibok” dalibai sama da 200 da kungiyar Boko ta sace a wata makaranta a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin kasar a shekarar 2014.

Kusan rabin wadanda lamarin ya shafa ba’a same su ba, wadanda aka kirkiri maudu’in #BringbackOurGirls, lamarin da ya sa yanzu aka kirkiri #BringBackOurBoys.

Usama, ya ce 'yan bindigar na Katsina, sun yi ta takatsantsan kada a gano su, lamarin da ya sa suka raba daliban zuwa gida-gida. Ya ce yana cikin rukuni na kusan dalibai 50, tare da ‘yan bindiga hudu a gabansu, yayin da sauran suke tafiya a gefen sauran daliban. Sun yi tafiyar sa’o’i tare kuma sun tilastawa dalibai manya su dauki wadanda suka gaza.

Zagi da cin mutunci ya sa tafiyar da suke yi ta yi wahala sosai. Usama ya ce game da masu garkuwar “Sun ci gaba da dukan mu yayin da muke tafiya.”

“Babu abinci, wannan yasa muka rika tsinkar kayan itatuwa da ganye daga kowace bishiya. Na gaji sosai kuma bana iya tsayawa, dan haka sauran daliban sai su kawo mini ganye na ci. Ganyen kan sa mutum jin kishin ruwa, kuma babu ruwan da mutum zai sha.”

Usama ya ce daliban sun ci gaba da tafiya a cikin daren ranar Asabar. “Bayan mun yi tafiya na lokacin mai tsawo, sun ce mana mu durkusa akan gwiwowin mu yayin da suke jiran sauran daliban su zo.” sai daga baya ya fahimci cewa akwai wani kauye a kusa.

“Na yanke shawarar inda zan kwanta saboda ina cikin matsanancin ciwo,” inajin kasusuwana suna ciwo. “Ba zan iya cigaba da tafiya ba. Ina fada a raina, ina iyayin sa’a su barni a baya, sai na fara addu’a.”

'Yan bindigar sun ta kokarin kaucewa kar a gano su, suka cigaba da tafiya a cikin duhu kuma basu lura da cewa Usama bayan nan ba.

Usama ya ce bayan da sauran suka tafi, sai ya samu karfin gwiwa da zai tunkari masallaci a kauyen. Da gari ya waye, sai wani yazo ya shiga ciki, sai Usama ya yi tari don ya dauki hankalinsa. Bayan an idar da sallah, sai mutumin ya kawo masa kaya ya daura kan kayan makarantarsa, sanann ya biya masa kudin mota don ta kai Usama wurin iyayensa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara aikin kokarin ceto daliban a ranar Asabar. Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Abdu Labaran, a ranar Litinin ya fadawa gidan talabijin na CNN cewa, akalla dalibai 446 sun koma hannun iyayensu. Har yanzu ba a bayyana iya yara nawa ne suka bataba.

Your browser doesn’t support HTML5

Iyaye Sun Bayyana Fargabarsu Kan Garkuwa Da Daliban Najeriya

Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, da jihar Katsina.