‘Yan sanda a jihar Zamfarar Najeriya, sun kubutar da biyu daga cikin daliban sakandare Yauri da ‘yan bindiga suka sace sama da mako shida da suka gabata a jihar Kebbi.
A ranar 17 ga watan Yuni ‘yan bindigar suka far wa makarantar sakandaren Yauri suka sace dalibai da dama.
Hukumomin tsaro a jihar sun tabbatar da sakin daliban, sai dai babu wasu bayanai da suka nuna ko an biya kudin fansa.
Wakilin Muryar Amurka a Zamfara Sani Shu’aibu Malumfashi ya ce yanzu haka daliban makarantar sakandaren birnin Yauri biyu da jami'an tsaro suka ceto a jihar Zamfara sun Isa jihar Kebbi kuma ana ci gaba da duba lafiyar su kafin daukar mataki na gaba.
“Muna so mu shida maku cewa, game da wadannan yara dalibai ‘yan makaranta da aka sace a Yauri, da iznin Allah jami’an tsaro da suke Dan Sadau, sun samu nasarar ceto yara biyu daga ciki wadannan da aka sace a Yauri.” In ji Kwamishinan ‘yan sanda a jihar ta Zamfara Hussaini Rabiu.
Yanzu haka dai wadanda suka sace daliban na ci gaba da rike yaran da adadinsu ba zai kasa tamanin ba.
A baya dai an yi nasarar kubutar da biyar daga cikin daliban sai kuma wadannan da aka kubutar a ranar Asabar.
Rahotanni sun ce an kubutar da daliban ne a dajin da ke Gundumar Dan Sadau a karamar hukumar Maru da jihar Zamfara.
Sakin daliban na zuwa ne yayin da arewa maso yammacin kasar ke fama da masu satar mutane don neman kudin fansa, lamarin da ya sa aka rufe makarantu da dama a yankin.
Gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu ya sha alwashin hada gangamin da zai shiga daji don kubutar da daliban wadanda suka hada da mata da maza.
Gabanin satar daliban na Yauri, wasu ‘yan bindiga na daban a jihar Neja sun sace daliban wata makarantar Islamiyya sama da 100
Your browser doesn’t support HTML5