Yadda Dalibai Suka Rasa Rayukansu a Bauchi

Bauchi

Wani ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar rasa rayukan wasu dalibai hudu na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, a arewa maso gabashin Najeriya.

Daliban sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke tafiya akan wata gada, wacce ta karye bayan da aka tafka ruwan saman.

Akalla dalibai 40 ne ke tafiya akan gadar a lokacin da hadarin ya auku, inda rahotanni ke nuni da cewa, ba a ga wasu daga cikinsu ba.

A halin da ake ciki dai hukumar gudanarwar jami’ar ta rufe makarantar kamar yadda mataimakin shugabanta, Farfesa Muhammad Ahmad Abdulazeez, ya bayyana.

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammed, Kauran Bauchi, wanda ke kasar Saudiya ya jajanta wa al’ummar jihar, dangane da wannan al'amarin.

Ya kuma ba da umurnin da a dauki matakai domin shawo kan matsalar, da kuma kai kayan agaji ga mutanen da suka samu raunuka.

Shi ma Kakakin gwamnan Bauchin, Dokta Ladan Salihu, shi ma ya jajanta wa iyalai da al'umar Bauchi bisa wannan rashi.

A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Dalibai Hudu Suka Rasa Rayukansu a Bauchi