Kwanaki 10 bayan da aka gano bullar cutar coronavirus a Jamhuriyar Nijar hukumomin lafiyar kasar sun ba da sanarwar rasuwar daya daga cikin mutum 7 din da suka kamu da cutar.
Lamarin dai tuni ya fara jefa jama’a cikin zullumi.
Wata sanarwa da ma’aikatar kiwon lafiya ta fitar a kasar, ta nuna cewa dukkan mutanen da suka kamu da cutar ‘yan Nijar ne wadanda suka dawo daga Faransa a cikin watan nan na Maris.
Wanda cutar ta yi ajalinsa dai wani dattijo ne mai shekaru 63 kuma ya rasu ne a babban asibitin Yamai inji sanarwar.
Wannan lamarin dai ya zama tamkar wata manuniya ga ‘yan kasar da ke ci gaba da nuna halin ko in kula da matakan riga kafin da hukumomi suka shimfida.
A wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar shugaban kasa Issouhou Mahamadou, ya ce an dauki matakai da dama na wucin gadi wadanda suka hada da rufe iyakoki na sama da makarantun boko da gidajen wasanni da na nishadi yayin da aka yi gargadi jama’a su takaita shagulgulan aure da suna kafin daga bisani a rufe tashoshin shiga motocin jigila.
Ga cikakken rahoton a sauti.
Your browser doesn’t support HTML5