Yadda Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa

Hukumomi na cewa suna ci gaba da tattara bayanai dangane da harin da mayakan Boko Haram suka kai a garin Garkida da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.

'Yan ta'addan sun kai farmakin ne da misalin karfe 7 bayan sallar Magariba a a daren Jumma’a, inda suka yi ta harbin kan-mai-uwa-da-wabi.

Rahotannin sun ce 'yan ta’addan sun shiga cikin garin ne da motoci tare da bat da kama ta hanyar yin shiga irin ta sojoji.

Garin Garkida na da nisan kimanin kilomita 167 daga Yola, babban birnin jihar ta Adamawa.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce sojojin da ke garin wadanda ba su da yawa sun yi artabu da ‘yan ta’addan.

Bayanai sun yi nuni da cewa, wannan ya bai wa mayakan damar bazama cikin garin inda suka yi ta harbe-harbe da kuma bankawa gidaje wuta.

Tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Adamawa, wanda dan asalin garin Garkida ne, Mr. Andrawus Terfa, ya ce sun tsinci kansu a cikin rudani yayin da ‘yan Boko Haram din suka kai harin.

Ya zuwa yanzu rundunan soji ta 23 da ke Yola, ba ta yi karin haske dangane da harin ba.

Amma kakakin rundunan ‘yan sandan jihar DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya ce, suna iya kokarinsu don ganin sun hada bayanan abin da ya faru.

‘Yan Boko Haram sun kara zafafa kai hare-hare a cikin kwanakin nan a wasu yankunan jihohin Adamawa, Borno da Yobe.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Boko Haram Ta Kai Hari a Adamawa