Yadda Aka Yi Bikin Ranar Dimokradiya Karo Na 30 a Nijar

Jama'a a wajen taron dimokradiyya a Nijar

A Jamhuriyar Nijer yau ake bukin raya ranar dimokradiya wace ta samo asali daga babban taron mahawarar kasa na ranar 29 ga watan yulin 1991 wanda ya kawo karshen mulkin soja na tsawon shekaru 16.

A albarkacin wannan rana wasu daga cikin wadanda suka halarci wannan taro sun shirya zama a yau domin yin waywaye akan shawarwarain da aka tsayar a wancan lokaci.

Kwanaki kimanin 98 ne aka shafe ana tafka mahawara a tsakanin daruruwan wakilan kungiyoyi da jam’iyun siyasa da nufin zakulo matsalolin da suka dabaibaye al’amura a wancan lokaci a matsayin wani matakin share fagen dora jamhuriyar Nijer akan turbar dimokradiya saboda haka shekaru 30 bayan wannan zama aka shirya taro domin bitar shawarwarin da aka tsayar.

Shugaban jam’iyar PNA Al’umma Sanoussi Tambari Djakou na daga cikin wadanda suka taka rawa a taron na 1991. Ya ce Conference Nationale ita ce ta dauke 'yan nijar da ake kira talakawa, ta mai da su 'yan kasa masu yancin kansu.

Taron mahawarar ya kasance tamkar wani juyin juya halin da ya karbe madafun iko daga hannun sojojin da suka shafe shekaru 16 akan karaga. la’akari da karfin guguwar da ta taso a 1991 ya sa shugaban kasa General Ali Chaibou ba da kai ba tare da wata wata ba.

Matasa kamar Mohamed Sidi, na fatan samun darasi daga abubuwan da suka faru a yayin taron na Conference Nationale dalili kenan da ya sa suka hallara a wurin wannan zaman bita.

Mahawarar kasa wato Conference Nationale ta kasance wata garkuwar da ta baiwa ‘yan kasa sukunin morar ‘yancin fadin albarkacin baki abinda ya sa ake kiranta babban gwadabe kuma dukkan shugabanin da suka mulki Nijer daga November 1991 kawo yau sun bi ta nan.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Aka Yi Bikin Ranar Dimokradiya Karo Na 30 a Nijar