Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ziyarci Najeriya don tunawa da ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya da suka rasa ransu a harin ‘yan ta’adan da aka ofishin majalisar da ke Abuja a shekarar 2011.
Ma’aikatan majalisar 23 ne suka rasa rayukansu, wasu 116 kuma suka jikkata a lokacin da mayakan Boko Haram suka dasa bam a ofishin majalisar da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Dukkan mamatan ‘yan Najeriya ne, illa wata ‘yar kasar Norway ita kadai.
Guterres, ya kai ziyara Najeriya domin halartar taron tunawa da girmama ma’aikatan majalisar 23 da suka rasu.
Duk da cewa a ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2011 da misalin karfe 10 safe ne bam din ya tashi, Antonio Gutteres, ya shigo Najeriya don halartar taron na musamman na tunawa da mutanen da lamarin ya rutsa da su da alamar girmamawa.
Bayan shigowar Gutteres da misalin karfe 9 da wasu mintuna, ma’aikatan majalisar sun shiga wani taro cikin sirri domin tattauna batutuwa kan abin da ya kawo su.
Guteres dai na ziyarar aiki na kwanaki hudu ne a kasashen Afirka da suka hada da Senegal, Jamhuriyar Nijar, da kuma Najeriya inda ya ziyarci jihar Borno ya gana da gwamna Farfesa Babagana Zullum, iyalen wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su da ma wasu tubabbun ‘yan Boko Haram.
Kungiyoyin mata, matasa, da bangaren da ba na gwamnati ba a Najeriya na daga cikin mutane da suka gana da Gutteres a ofishin majalisar dinkin duniya dake unguwan diplomatic drive da ke birnin tarama Abuja.