Kimanin mutum 16 ‘yan bindiga suka halaka a wasu kananan hukumomi jihar Filato biyu a daren Lahadi.
Bayanai na nuni da cewa mutum takwas ne ‘yan bindigar suka halaka a yankin Dong dake karamar hukumar Jos ta Arewa yayin da wasu mutum takwas ‘yan bindigar suka halaka a kauyen Kwi dake karamar hukumar Riyom.
Barista Solomon Dalyop ya ce ‘yan bindigar sun far ma kauyawan ne yayin da suke bacci.
“Akwai mutum biyar kuma da aka kashe wadanda suka je jana’izar mutum takwas a Dong.” Dalyop ya ce.
Karin bayani akan: Alhaji Nura, jihar Filato, Fulani, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Al’umar yankunan da hare-haren suka shafa, na zargin Fulani da aikata wannan ta’asa.
Sai dai Shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar ta Filato, Alhaji Nura Muhammad ya ce a cikin ‘yan kwanakin nan a kashe masu yara makiyaya da dabbobinsu.
“Mu ma an kashe mana yara, daya biyu, daya biyu, wannan abubuwan ba za su taimaka mana ba, mafita ita ce a hadu da jami’an gwamnati da jami’an tsaro da mu da su a zo a zauna a kalli idon kowa a fadi gaskiya.” Muhammad ya ce.
Kwomishinan yada labarai da sadarwa a jihar Filato, Mr. Dan Manjang ya ce tuni aka dauki matakan takaita wanzuwar rikicin.
“Kura ta lafa a yanzu, an sa jami’an tsarosun je sun tsayar da wannan tarzoma. Babban kira shi ne, manoma su kiyaye dabbobin makiyaya, makiyaya su kiyaye gonakin manoma.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, ASP Gabriel Uba, ya tabbatar da mutuwar mutum bakwai ne a yankin na Dong inda ya ce ba su kama kowa ba amma suna kan gudanar da bincike.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5