Marigayi Chadwick Boseman ya lashe lambar yabo da ya samu a karon farko a bikin, a fim din “Ma Rainey’s Black Bottom.”
Boseman ya samu kyautar ne a matsayin jarumin da ya fi fice a rukunin fim na fina-finai, kuma matarsa Simone Ledward ce ta karbi kyautar a madadinsa.
Jarumin na “Black Panther” ya rasu ne a watan Agustan bara yana mai shekara 43 bayan da ya fama da cutar sankarar babban hanji.
Bikin wanda aka yi shi a karo na 78 ya kunshi ba da lambobin yabo ga fina-finan da suka yi zarra a taron wanda ya gudana a jiya Lahadi.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa an karrama fim din “Nomadland” a matsayin fim na drama da ya fi kowanne sannan aka karrama darekta Chloe Zhao a matsayin wacce ta yi fice a tsakanin takwarorinta.
A gefen fina-finan barkwanci, fim din “Borat Subsequent Moviefilm” ne ya fi kowanne, sannan an ba Sacha Baron Cohen a matsayin wanda ya fi kowa iya wasan na barkwanci.
Shi kuwa fim din “The Crown,” ya yi zarra a matsayin wasan kwaikwayon na talbijin da ya fi fice.
Tina Fey da Amy Poeler da suka kware a fannin wasan barkwanci ne suka gabatar da bikin, wanda shi ne babban taron na karrama jarumai da fina-finai da aka gudanar a wannan zamani na annoba.
Sauran karramawa da aka yi sun hada da:
Jarumar da tafi kowa iya wasan kwaikwayo – Andra Day, wacce ta samu lambar yabo da fim din “The United States vs Billie Holiday.”
Jarumi da ya fi kowa iya wasan kwaikwayo a fannin barkwanci: Sacha Baron Cohen, wanda ya samu kambun da fim din “Borat Subsequent Moviefilm”
Jarumar da ta yi fice a iya wasan barkwanci: Rosamund Pike, da fim din “ I Care A Lot”
Sai fim din “Minari” da ya samu lambar yabo a matsayin fim din da ya yi fice a fina-finan kasashen waje da aka yi da wani harshe