Yadda Aka Gudanar Da Zanga Zanga Kan Albashi Mafi Karanci a Filato

Zanga zangar mafi karancin albashi a jihar Filato

Kungiyoyin ma’aikatan kananan hukumomin jihar Filato sun fada wani sabon zanga-zanga don jan hankalin gwamnati ta biya su albashi mafi karanci na Naira dubu talatin.

Daukacin Ma’aikatan kananan hukumomin jihar Filato 17 da suka hada da ma’aikatan jinya, malaman makarantun firamare, ungozoma da masu jinya ne suka sanya bakaken tufafi rike da kwalaye a kan tituna da ke cewa “mun gaji da karba rabin albashi tun shekaru tara’’, “albashinmu ba zai sayi buhun shinkafa ba’’ da sauransu.

Shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya a karamar hukumar Jos ta Arewa, Mr. Peter Davou Pam, ya ce sun gaji da Abin da ya kira yaudara da gwamnati ke yi musu tun shekarar 2012.

Ita ma Rejoice Adams daga karamar hukumar Jos ta Gabas ta ce zanga-zangar da su ke yi suna bukatar shugaban kasa da ‘yan majalisu ne su dauki matakin biyansu albashin naira dubu 30.

zanga zanga mafi karancin alabashi a jihar Filato

Wata malamar makaranta Madam Elizabeth Bitrus, ta ce sheraka tara da ta wuce an ba da mafi karancin albashi Naira dubu 18 ba’a basu ba, kwatsan yanzu sai ga wannan karin albashi ya zo yanzu kuma gwamanatin ta ce ba ta da kudi.

Madam Elizabeth ta kara da cewa wai idan abin yazo kan malama makaranta ne ake cewa babu kudi kuma za su cigaba da yin zanga zangar.

A bangaren gwamnati kuwa, shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa, Shehu Bala Usman, ya ce tun da abin ya riga ya zama doka, yanzu haka an kafa kwamiti da ya hada da kungiyar kwadago da shugabanin kananan hukumomi don fito da tsarin biyan albashin kuma suna basu hakuri.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar mafi karanci albashi ta 2019 a ranar 18 ga watan Afrilun, 2020, inda dokar ta fara aiki nan take.

Sai dai har yanzu wasu jihohi da ma'aikatun masu zaman kansu sun yi biris da wannan doka ta mafi karnacin albashi na Naira dubu talatin, inda suke ku kan basu da isassun kudi domin biyan ma'aikata.

A baya dai irin wannan zanga zangar takan rikide ta zama ta tashin hankali muddin gwamnati ba ta dauki mataki ba.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Aka Gudanar Da Zanga Zangar Albashi Mafi Karanci a Filato