A yau Amurka ta ke cika shekara 244 da samun 'yancin kai, amma a wannan shekarar an gudanar da bikin tunawa da ranar ne ba yadda aka saba ba.
Yawancin Amurkawa sun kasance zaune a gida kawai, sabanin yadda aka saba shagulgula a kowace ranar idan shekara ta zagayo.
Ranar da ake kira "4th of July" ta fado a dai-dai lokacin da mutane a Amurka ke kara kamuwa da cutar Coronavirus.
Lamarin da ya janyo gwamnoni da dama a kasar suka mayar da dokokin takaita zirga-zirgar da aka fara sassautawa.
A kowace shekara Amurkawa sun saba fita fareti sanye da tufafin da suka yi dai-dai da kalolin taswirar Amurka.
A babban birnin kasar ta Amurka, Washington DC yanayin Covid-19 bai hana shugaba Trump shirya wani taro inda mutane zasu samu damar kallon shawagin jiragen soji da sauransu.
Tun safiyar yau dai mutane suka fara taruwa a wurin da za a gudanar da taron duk da cewar Magajiyar garin ta Washington DC ta yi wa mutane gargadi kan zuwa tarurruka domin kaucewa yaduwar cutar.